Daga Rumasau Muhammad Idris
A karon farko, malaman Jami’ar Ilimi ta Tarayya dake kano sun kaddadamar da sabuwar kungiyar ASUU.
Wannan na kun she a cikin wata takardar bayan taron da a ka rabawa manema labarai mai dauke da sa hannun shugaban taron Abdulkarim Ahmad Tijjani.
A yayin taron, an cinma matsayar shugabancin kungiyar, inda mahalarta taron suka zabi Dakta Bashir ibrahim a matsayin shugaba.
Yayin da aka zabi Dokta Aliyu Yaya Aliyu amatsayin sakatare da kuma sauran masu taimakusu kamar yadda sanarwa ta bayyana.
Haka kuma an cinma matsaya akan wasu bukatun malaman jami’ar, inda aka mika su ga gajorancin makarantar domin tunkarar kalubalen da ke fuskantar su.
Daga karshe an yanke shawayar gayyatar sauran malaman jami’ar dake sha awar shiga kungiyar domin zama manbobi tare da yunkurin samarda kundin tsarin da fiyar da kungiya,