Argentina ta tsallaka zuwa wasan kwata-fainal na Gasar Kofin Duniya na 2026, bayan sun yi nasarar doke Masar da ci 3-2 a wasan da aka yi karon-batta tsakanin ƙasashen biyu a zagayen ’yan 16.
Masar ta bai wa duniya mamaki bayan da Yasser Ibrahim ya jefa ƙwallon farko a minti na 15, sannan Lionel Messi ya ɓara da fenariti a minti na 21.
A minti na 67, Mostafa Zico ya ƙara jefa ƙwallo ta biyu a ragar Argentina, wanda hakan ya sa Masar takusa da samun nasarar tarihi kan zakarun duniya.
Sai dai Argentina ta nuna bajinta da ƙwarewa a mintunan ƙarshe na wasan.
Cristian Romero ya warware ƙwallo ɗaya s minti na 79 bayan bugun kusurwa da Messi ya bugo, daga baya kuma Messi ya sake warware ƙwallo ta biyu a minti na 83.
A lokacin da ake tunanin za a tafi ƙarin lokaci, Enzo Fernández ya zura wa Argentina ƙwallon da ta ba su nasara a minti na 93.
Wannan sakamako, ya bai wa Argentina damar tsallakawa zuwa wasan kwata-fainal.
Ita kuwa Masar ta fice daga gasar duk da rawar gani da ta taka.

