Kotun Dake sauraron shari’ar Dakatacen Gwamnan Babban Bankin Kasa CBN, Godwin Emefele, ta Bayar Da Belinsa Bisa wasu sharudai.
Kotun Ta ce Ya zama Wajibi ya Ajiye Kudi naira Miliyan 20 Da kuma Mutum Guda Da zai tsaya masa Wanda Kuma shi ne zai Biya wancan Kudi.
An gurfanar da gwamnan Babban Bankin na Najeriya, Godwin Emefiele da aka dakatar, a gaban wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas a safiyar yau Talata bisa zargin aikata laifuka biyu da suka hada da mallakar makamai da alburusai ba bisa ka’ida ba.
Emefielen ya gurfana ne a gaban mai shari’a Nicholas Oweibo, bayan shafe sama da makonni shida da kama shi da hukumar DSS ta yi