Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya gargadi kungiyar ECOWAS kan afkawa Nijar da yaki.
El-Rufai ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a yau Talata. Inda yake cewa Nijar ‘yar’uwar Arewacin Najeriya ce.
Nasiru El-Rufai ya kasance na kusa da shugaban kasa, Bola Tinubu inda ya shawarce shi kan matakin soji da kungiyar ECOWAS ke son dauka kan Jamhuriyar Nijar.
Ya kara da cewa Shugaba Tinubu a matsayinsa na jagoran kungiyar ECOWAS ya kamata “ya guji wannan yaki tsakanin ‘yan’uwan juna. Saboda haka, ya kamata mu kaurace wa wannan yaki na koma baya tsakanin ‘yan uwa.
Idan ba a manta ba sojin kasar Nijar sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum ne a karshen watan Yuli kan wasu korafe-korafe a kansa.
Kungiyar ECOWAS a baya ta saka wa kasar Nijar takunkumi bayan sojin kasar sun yi fatali da umarninta