Kungiyar Kwadago ta ƙasa ta nuna rashin gamsuwar ta da karin farashin man fetur zuwa N617, inda ta ce wannan lamari sam bai wa ƴan najeriya dadi ba.
A yayinda yake mayar da martani game da karin farashin, babban jami’in yada labarai da harkokin jama’a na kungiyar, Kwamared Benson Upah, ya shaida wa majiyarmu cewa, karin farashin babbar barazana ce ga rayuwar al’umar ƙasar nan dama tattalin arzikinsu.
Ƙungiyar ta ƙwadugo ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sake duba matakanta na kudirin kai farashin man fetur zuwa Naira 1,000 na kowace lita.
Ya ce, har yanzun kungiyar ba ta gamsu da cewa, cire tallafin man fetur din zai amfanar da jama’a ko tattalin arzikin kasa ba, ko kuma cewa, cire tallafin zai sake karfafa guiwar ‘yankasa kan samun sabuwar rayuwa mai inganci.