Shugaban rukunin kamfanin man fetur na ƙasa, Mele Kyari, ya ce yanayin kasuwar man fetur ce tasa farashin man ya ƙaru izuwa Naira 617.
Kyari ya bayyana haka ne a yammacin jiya talata, bayan ganawarsa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Ya ce idan aka karkata akalar man fetur, hakikanin kasuwa zai sa farashin man fetur ya tashi a wasu lokutan, wani lokacin kuma yasa ya sauka.
Shugaban kanfanin man, ya ce karin farashin man na kowace litar daga sama da N500 zuwa N617 ba batun karancin sa ba ne, yana mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Nigeria na da wadataccen man a kasa yanzu haka.
Kyari ya ce tawagar harkokin kasuwanci ta kanfanin man ce ke da alhakin daidaita farashin kuma ayarin zai “daidaita farashin daidai da yanayin da kasuwa ta nuna.