Kungiyar Malaman Kwalejin Ilimi ta ƙasa COEASU ta umarci dukkan mambobinta da su riƙa zuwa aiki na kwanaki biyu kacal a sati.
Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Smart Olugbeko ne ya bayyana haka a yau Laraba 19 ga watan Yuli, a birnir tarayya Abuja, Inda ya bayyana cewar, wannan mataki ya biyo bayan ganawar da mambobin kungiyar suka yi ganin halin da ake ciki a kasar bayan cire tallafin man fetur.