Kungiyar Sure4u ta bayar da gudnmawar kayan da za su taimakawa marasa lafiya, a babban asibitin garin Hadejia dake Jihar Jigawa, don kara inganta harkokin lafiyar al’umma.
Jakadiyar SURE4U, Ambasada Bilkisu Babandede, ita ce ta mika kayan ga asibitin, har ta bayyana cewa a koda yaushe kungiyar tana yin hangen nesa dangane da Koken al’umma musamman abinda yafi damun su domin warware musu matsalolinsu.
Wasu daga cikin kayan da suka bawa asibitin sun hada da keken tura marasa lafiyan da baza su iya zama ba guda 2, da kujerar da ake dora wadanda basa iya tafiya guda 5 da kuma abin auna jinin mara lafiya guda 20.
Ta kara da cewa burin SURE4U shi ne farantawa al’umma rai, domin ba yanzu kungiyar ta fara bayar da irin wannan gudunmawar ba, domin kuwa zuwa yanzu sun yi abubuwa masu yawa.
- Kwayar Colorado Ta Kashe Dan Shekara 43 A Kwara Yayin Bikin Sallah
- An Gurfanar Da Mutane 29 A Gaban Kotu Bisa Zargi Kashe DPO A Kano
Kungiyar dai tana tallafawa marayu da kuma matan da mazajensu suka rasu.
Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan kungiyar ta dauki nauyin karatun marayu 50 a masarautar Hadejia.
Shugaban ma’aikatan lafiya na babban asibitin Hadejia, Dr. Saleh A. Umar, ne karbi kayan a madadin shugaban asibitin, inda ya mika godiyarsu ga kungiyar SURE4U bisa gudunmawar da take basu a koda yaushe..
Ya kara da cewa ba wannan ne karon farkon ba da kungiyar ta taba basu irin wannan tallafi ba, domin duk wanda yake Hadejia yasan da hakan.
A karshe an kungiyar da kuma ma’aikatan asibitin, sun yi addu’o’I da kuma yiwa juna fatan alkairi.