• Home  
  • Za Mu Bai Wa Manoma Cikakken Tsaro: Bello Matawalle 
- Babban Labari - Labarai

Za Mu Bai Wa Manoma Cikakken Tsaro: Bello Matawalle 

Ƙaramin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya ce suna bai wa manoma tabbacin samun isasshen tsaro da zai basu damar komawa gonakinsu gabanin daminar bana domin bunkasa harkokin noma

'Yan Sanda Sun Kai Samame Tare da Kwashe Motocin Alfarma a Gidan Tsohon Gwamnan Zamfara

Ƙaramin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle ya ce suna bai wa manoma tabbacin samun isasshen tsaro da zai basu damar komawa gonakinsu gabanin daminar bana domin bunkasa harkokin noma

Ministan ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a garin Maradun, Zamafara, a jiya Lahadi.

Ya ce, an tura jami’an tsaro dazuzzuka domin tabbatar da tsaron filayen noma, kuma ana amfani da fasahar zamani wurin gudanar da aikin.

Ya ce “Muna daukar dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da cewa manoma sun koma gonakinsu lafiya tare da cikakkiyar kariya daga duk wata barazanar tsaro a fadin kasar nan,”

Ya kara da cewa, gwamnatin kasarnan na shirin samar da tsarin tsaro na ‘yan asalin yankunan da za su yi aiki domin tunkarar kalubalen tsaro da kuma iya samar da su ga wasu kasashe.

Matawalle ya bukaci gwamnoni su ba da tallafin kayan aiki da suka hada da masauki, motocin aiki, da tattara bayanan sirri, don taimakawa wajen tabbatar da tsaro a yankunan karkara.

Ministan ya ce wasu gwamnonin na yin wasan zargi maimakon goyon bayan kokarin gwamnatin tarayya na magance matsalar rashin tsaro. Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta ruwaito

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai