Mazauna yankin Edun da ke Ilorin sun tsinci kansu cikin tashin hankali jim kadan bayan sallar Idi ranar Juma’a sakamakon wani mutum mai suna Kazeem dan shekara 43 ya faɗa a rijiya sakamakon shan kwayar Colorado.
Rahotanni sun ce Kazeem ya sha ƙwayar ne a bikin idi.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan da Kazeem ya dawo daga Sallar Idi, lamarin da ya haifar da kaduwa da rudani a tsakanin al’ummar yankin.
- An Gurfanar Da Mutane 29 A Gaban Kotu Bisa Zargi Kashe DPO A Kano
- Kisan DPO Rano: Yan Sanda Sun Gano Bindiga AK-47 Ta Bogi A Gidan Wanda Ake Zargi
A wata sanarwa da hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta fitar, hukumar ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:29 na safe daga unguwar Alapo da ke Edun, inda aka sanar da su ga wani mutum ya fada rijiya.
Kakakin hukumar kashe gobara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin. In da ya ce, sun samu kiran gaggawa daga unguwar su Kazeem, sai dai ko da suka iso rai ya riga ya yi halinsa.