Kwamishinan labarai da al’adu na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya buƙaci jami’an yaɗa labarai da ke ƙananan hukumomi arba’in da huɗu da kan su ƙara mayar da hankalin wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.
Kwamishinan ya yi wannan kira ne a yayin wani taro da jami’an da ke dakin taro na ma’aikatar.
Ya kuma buƙaci su yi amfani da dabaru na musamman wajen yaɗa labaran ayyukan da gwamnatin jihar Kano ta fara yi a ƙananan hukumomin da ke jihar nan.
Sannan ya ja hankalinsu kan cewa ayyukansu ba sun tsaya ne kawai ga ba da labarin ayyukan da ciyamomin ƙananan hukumominsu ke yi ba.
A cewarsa jami’an ya kamata su riƙa ba da rahoto game da ƙalubalen da su hukumomin nasu ke fuskanta da ke buƙatar gwamnati ta ɗau mataki na gaggawa.
A ƙarshe, kwamishinan ya tabbatar wa da jami’ansa cewa za a kula da walwalarsu.