• Home  
  • Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.
- Labarai

Kwamitin zaman lafiya ya gana da yan sandan Kano kan zaɓen 2027.

Kwamitin zaman lafiya na kasa ya ziyarci rundunar yan sandan jihar Kano domin tattaunawa kan matakan da za a ɗauka wajen tabbatar da zaman lafiya a zaɓen 2027. Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata. Sanarwar […]

Kwamitin zaman lafiya na kasa ya ziyarci rundunar yan sandan jihar Kano domin tattaunawa kan matakan da za a ɗauka wajen tabbatar da zaman lafiya a zaɓen 2027.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta ce twagar, wadda Mista Espom Ajanya daga Cibiyar Kukah ya jagoranta, ta ce tana gana wa da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tantance yanayin tsaro da kuma abubuwan da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya yayin zaɓen.

Tawagar ta kuma yaba da matakan da rundunar yan sandan Kano ke ɗauka wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce ziyarar ta zo a kan lokaci, yana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne zaman lafiya.

Ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da su guji duk wani abu da zai iya haifar da tashin hankali kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.

Kwamishinan ya ce rundunar a shirye take ta yi aiki tare da INEC, sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin aminci da lumana.

Ya ce tuni rundunar ta fara horas da jami’anta kan tsaron zaɓe, tare da ƙarfafa tattara bayanan sirri da wayar da kan jama’a.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai