• Home  
  • Kwastam Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira Miliyan 5 A Legas
- Babban Labari - Labarai

Kwastam Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira Miliyan 5 A Legas

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta kama miyagun kwayoyin da aka kimanta darajarsu zuwa Naira millyan ɗari biyar da sittin da biyu a yankin Gbaji na Badagryn  Jihar Legas. An gano kwayoyin ne a lokacin wani aikin bincike da jami’an Zone A, Ikeja, suka gudanar a kan hanyar da ta kai iyakar Seme. Kwamandan Sashen, Mohammed […]

Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta kama miyagun kwayoyin da aka kimanta darajarsu zuwa Naira millyan ɗari biyar da sittin da biyu a yankin Gbaji na Badagryn  Jihar Legas.

An gano kwayoyin ne a lokacin wani aikin bincike da jami’an Zone A, Ikeja, suka gudanar a kan hanyar da ta kai iyakar Seme. Kwamandan Sashen, Mohammed Shuaibu, ya bayyana haka a ofishinsa.

A cewar Kwamandan, an kama kayan ne, lokacin da wata tawagar sintiri, sakamakon wasu bayanan sirri, ta kamo wani mutum mai suna Uduak Monday.

Ya bayyana cewa an sami wanda ake zargin dauke da wata jaka, wadda bayan an bincika, aka gano wani sinadari a ciki mai suna Ice Crystal Methamphetamine mai nauyin kilogiram 25, wanda aka kimanta darajarsa a kasuwa zuwa Naira miliyan ɗari biyar da sittin da biyu cikin ɗari biyu.

Ya kuma bayyana cewa, an mika sinadarin da aka kama ga Hukumar Yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) domin gudanar da ƙarin bincike da kuma gurfanar da wanda ake zargi.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000