Gwamantin Jihar Adamawa ta tabbatar da ta ƙwace ikon naɗa wa da tsige sarakuna daga hannun Lamiɗon Adamawa, Alhaji Mustapha Barkinɗo ta damƙa wa Gwamnan Jihar.
Haka zalikaɓgwamnatin ta tsige Lamiɗo daga matsayinsa na Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar na dindindin.
Majalisar Dokokin Adamawa ce dai ta yi wa dokar masarautun jihar garambawul a ranar Laraba, haka kuma ta rage ƙasar Masarautar Lamiɗon Adamawa daga ƙananan hukumomi takwas zuwa uku: Girei da Jimeta da kuma Yola.
- Mai Shara Ya Mayar Da Miliyan 40 Da Ya Tsinta A Kano
- AKwai Mamaki Yadda Ganduje Ya Kasa Biya wa Ɗalibai Kuɗin Makaranta-AKY
Dokar, majalisar ta ce za ta tabbatar da adalci a tsakanin masarautun jihar da kuma kare tarihi da al’adu.