Wani mai sharar asibiti a Kano da ake kira Malam Aminu Umar Kofar Mazugal ya mayar da kudin da ya tsinta da suka kai kimanin Naira miliya 40 ga mai su.
Malam Aminu ya tsinci kudin ne a dalolin Amurka a cikin wata jaka da mai su ya manta a Asibitin Abubakar Imam da ke unguwar Fagge a cikin birnin Kano.
Ya tsinci kudin a cikin wata jaka kuma ya mayar da kudin ga mai su, Alhaji Ahmed Abubakar, wanda ya manta da su a lokacin da ya je dubiyar mara lafiya a asibitin.
- AKwai Mamaki Yadda Ganduje Ya Kasa Biya wa Ɗalibai Kuɗin Makaranta-AKY
- Isra’ila Ta Kai Hare-hare 300 Syria
Malam Aminu ya shaida wa wakilinmu Aminiya cewa jim kadan da tafiyarsa mutumin ne shi kuma ya tsinci kudin a lokacin da yake aikin shara.
Ya ce daga bisani, bayan kimanin awa guda, mai kudin ya dawo yana cikiya, shi kuma ya mayar masa kayansa.
Shugaban Asibitin, Dokta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa hukumar gudanarwar asibitin ta sanar da Ma’aikatar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano domin a karrama Malam Aminu.