A shirye-shiryen bude sashen talabijin na Muhasa baya ga sashen rediyo da tuni ya daɗe da fara aiki kan mita 92.3 a zangon FM, wasu daga cikin ma’aikatan wannan gida sun samu horo na musanman na sannin makamar aiki a bangaren talabijin.
Wannan wani mataki ne tabbatar da an samu ƙwarewa da kuma gabatar da ingantattun ayyuka ga al’ummar da ake yi dominsu.
Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa. Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.