• Home  
  • Mace ta farko ta fito neman takarar gwamnan Gombe a APC a zaɓen 2027.
- Babban Labari - Siyasa

Mace ta farko ta fito neman takarar gwamnan Gombe a APC a zaɓen 2027.

Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha, wadda aka fi sani da Alkyabbar Kaltungo, ta zama mace ta farko da ta shiga sahun manema takarar Gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027. Ta bayyana aniyarta ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga Afrilu, 2026, wadda Sakatariyar APC ta Jihar Gombe ta […]

Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha, wadda aka fi sani da Alkyabbar Kaltungo, ta zama mace ta farko da ta shiga sahun manema takarar Gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2027.

Ta bayyana aniyarta ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 16 ga Afrilu, 2026, wadda Sakatariyar APC ta Jihar Gombe ta karɓa a ranar 17 ga Afrilu, inda a ciki ta sanar da shugabancin jam’iyyar burinta na neman tikitin takarar gwamna.

Hajiya Sa’adatu, wadda ta shahara a fannin gudanarwa da kuma fafutikar kare haƙƙin mata, ta shafe shekaru ana damawa da ita a muhimman ayyukan gwamnati a jihar.

A baya, ta riƙe muƙamin Darakta-Janar ta Tsare-Tsare da Gudanarwa a Fadar Gwamnatin Jihar Gombe, inda ta jagoranci shirye-shiryen tarukan gwamnati da kuma tafiyar da muhimman ayyuka.

Haka kuma, ta taɓa zama Kwamishina a Majalisar Zartarwa ta jihar, inda ta bayar da gudumawa wajen tsara manufofin gwamnati musamman a fannonin ci gaba, ƙarfafa hukumomi da inganta ayyukan gwamnati.

Baya ga aikinta na gwamnati, Hajiya Sa’adatu ta kasance mai aikin wayar da kai da ƙarfafa mata, tare da horar da mata matasa kan shugabanci da muhimmancin shiga harkokin siyasa domin hidimta wa al’umma.

A cikin sanarwar da ta fitar, ta bayyana cewa burinta na neman kujerar gwamna ya samo asali ne daga ƙudirinta na bayar da gudumawa wajen ci gaban Jihar Gombe.

Ta yi alƙawarin mayar da hankali kan fannoni kamar ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi ga matasa da mata, bunƙasa tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa da kuma tsaro, idan aka ba ta dama.

Tuni dai bayan shigowarta sahun manema takara harkokin siyasa suka ƙara ɗaukar zafi, inda ake ganin hakan zai sa zaɓen 2027 ya ɗauki wani sabon salo, musamman la’akari da kasancewarta mace cikin ’yan takarar da ke neman kujerar gwamna.

Yayin da APC ke tunkarar zaɓen fidda gwani, ana sa ran fafatawa mai ƙarfi tsakanin masu neman tikitin jam’iyyar a jihar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai