• Home  
  • Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Abincin Buɗa Baki A Bauchi 
- Babban Labari - Labarai

Magidanci Ya Halaka Matarsa Kan Abincin Buɗa Baki A Bauchi 

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin yi wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Bauchi sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin yi wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.

An ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi.

Kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.”

’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar mai shekaru 24, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.”

Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci a lamarin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000