Wata tawagar kwararrun Majalisar Dinkin Duniya ta zargi jami’an gwamnatin Sudan ta kudu da hannu a azabtarwa da cin zarafi da kuma kisan tarin fararen hular da ya faru a sassan kasar.
Bayan samun ‘yanci daga Sudan a shekarar 2011, Sudan ta kudu ta fada yakin basasa bayan rikici da ya faro tsakanin Salva Kiir da Riek Machar wanda ya kai ga mutuwar mutane dubu dari 4 tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018 yayinda wasu miliyoyi suka tsere daga kasar zuwa makwabta.
Kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya sun ce kaso mai yawa na manyan jami’an gwamnatin Sudan ta kudu da suka aikata tarin laifukan cin zarafin bil’adaman har yanzu na rike da mukamansu a sassan kasar.
Sai dai tuni gwamnatin ta Juba ta mayar da martani inda ta bayyana bayanan kwararrun majalisar a matsayin masu shirin yi mata shisshigi a lamurranta na cikin gida.