• Home  
  • Majalisar Dattawan Amurka ta kaɗa ƙuri’ar haramta wa Trump yaƙi da Iran
- Babban Labari

Majalisar Dattawan Amurka ta kaɗa ƙuri’ar haramta wa Trump yaƙi da Iran

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wani ƙuduri da ke neman dakatar da duk wani sabon matakin soja kan Iran ba tare da sahalewar Majalisar Dokoki ba. Sanatoci 50 ne suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ƙudurin, yayin da 48 suka nuna adawa da shi. Sanatocin jam’iyyar Republican, Bill Cassidy na Louisiana, Susan Collins ta Maine, […]

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wani ƙuduri da ke neman dakatar da duk wani sabon matakin soja kan Iran ba tare da sahalewar Majalisar Dokoki ba.

Sanatoci 50 ne suka kaɗa ƙuri’ar goyon bayan ƙudurin, yayin da 48 suka nuna adawa da shi.

Sanatocin jam’iyyar Republican, Bill Cassidy na Louisiana, Susan Collins ta Maine, Lisa Murkowski ta Alaska da Rand Paul na Kentucky sun haɗu da ‘yan Democrat wajen goyon bayan ƙudurin.

Sanatan Democrat John Fetterman na Pennsylvania ya kaɗa ƙuri’ar ƙin amincewa da shi, yayin da Sanatocin Republican Mitch McConnell na Kentucky da Dave McCormick na Pennsylvania ba su kada kuri’a ba.

Ƙudurin ya buƙaci Shugaban Amurka, Donald Trump, ya janye sojojin Amurka daga duk wani farmaki ko rikici da Iran, sai dai idan Majalisa ta ba da izinin hakan a hukumance.

Sai dai ƙudurin ba ya buƙatar sa hannun shugaban ƙasa domin ya zama doka, kuma masana na ci gaba da muhawara kan irin ƙarfin doka da yake da shi.

An amince da wannan mataki ƙarƙashin Sashe na 5(c) na Dokar Ikon Yaƙi ta 1973 wanda tuni ya riga ya samu amincewa a Majalisar Wakilai.

A martaninsa, Trump ya soki matakin, yana mai bayyana ƙuri’ar a matsayin “abin da bai zo a lokacin da ya dace ba kuma mara ma’ana.”

Ya ce matakin ya ƙara masa wahala wajen tafiyar da manufofin gwamnatinsa kan Iran, amma ya jaddada cewa zai ci gaba da aiwatar da abin da yake ganin ya dace.

Ƙudurin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Trump ke ƙoƙarin cimma yarjejeniya ta dindindin da Iran kan shirinta na makamashin nukiliya, sassauta takunkumi da kuma makomar mashigin ruwa na Hormuz.

Shugaban masu rinjaye na jam’iyyar Democrat a Majalisar Dattawa, Chuck Schumer, ya ce ƙudurin na da nufin tabbatar da cewa Majalisa ta taka rawar da kundin tsarin mulki ya tanada wajen yanke shawarar shiga yaƙi.

Masu goyon bayan ƙudurin sun ce zai ƙarfafa bin tsarin dimokuraɗiyya da sa ido kan manyan matakan tsaro, yayin da masu adawa da shi ke ganin zai iya takaita ikon shugaban ƙasa wajen ɗaukar matakin gaggawa idan buƙatar hakan ta taso.

Muhawarar ta sake tayar da batun ikon shugaban ƙasa da na Majalisa wajen amincewa da ayyukan soja a ƙasashen waje, musamman bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Iran a watannin baya.

Babu tabbas kan tasirin aiwatar da wannan mataki a zahiri, tun da Washington da Tehran sun riga sun cim ma wata yarjejeniya ta wucin gadi ta zaman lafiya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai