Majalisar dattawan Najeriya ta yi wani zaman sirri kan tantance wani sanata mai suna Festus Keyamo.
Sanata Darlington Nwokocha ne ya fara gabatar da ƙudirin hakan a gaban majalisa, inda ya nemi a dakatar da shi har sai lokacin da ya amince da cewa majalisa na da damar bincikar ayyukan ministoci.
Hakan ya faru ne sakmakon tirjiyar da ya nuna a lokacin da yake minista a baya, inda ya ƙi amsa gayyatar majalisar.
Ƙudirin ya samu goyon bayan mafi rinjayen sanatoci, hakan ya sa daga ƙarshe majalisar ta yanke shawarar shiga zaman sirri kan lamarin.
Festus Keyamo ya yi minister a lokacin gwamnatin Buhari wanda kuma ya sake shiga cikin jerin sunayen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin minista.