A nan ma dai, Gwamnan jihar Barno, Babagana Zulum ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya guda 54 wanda za su ƙunshi mayan likitoci guda biyu, nas-nas guda takwas da kuma ungozoma da masu taimaka musu arba’in da biyu.
Daraktan lafiya kuma shugaban kula da asibitocin na jihar, farfesa Abubakar Ali Kullima, ne ya bayyana hakan a yayin ziyarar da ya kai babban asibitin da ke garin Gwoza .
Ya ce gwamnan jihar ya amince da hakan ne a wani ɓangare na cika alƙawarin da ya ɗauka na magance matsalar ƙarancin ma’aikatan lafiya domin wadatar da mutanen garin Gwoza.
A watan da ya wuce ne gwamnan ya kai wata ziyarar ba zata da daddare asibitin, inda ya tarar da asibitin ba wutar lantarki da tarin matsaloli.
Wanda daraktan ya tabbatar da shirin gwamnan na sake inganta gine-ginen asibitin.
Daga ƙarshe gwamnan ya yaba wa ma’aikatan waɗanda ke aiki a asibitin duk da irin mawuyacin halin da asibitin ke ciki.