Majalisar Dattawan Najeriya ta ki amincewa da yunkurin gwamnatin tarayya na amfani da karfin soji kan kasar Nijar.
Inda majalisar ta shawarci kungiyar ECOWAS da ta yi amfani da diflomasiyya wajen magance matsalar juyin mulki da sojoji suka yi a Nijar.
Wannan na zuwa ne bayan da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya aike wa da majalisar wasika game da aniyar ECOWAS na daukar matakin soji a kan kasar.
Sai dai bayan tattaunawa ta awanni biyu, majalisar ta amince da cewa ba su amince da daukar matakin soji ba a kan hafsoshin sojojin kasar ba.
Inda shugaban majalisar Godswill Akpabio ya ce shugabannin majalisar za su zauna da shugaba Tinubu kan cigaba da tattaunawa kan wannan al’amari.