Rahotanni sun tabbatar da wani hoton bidiyo wanda tsohon gwamnan ya yi wa Maryam Shetty shagube game da sanya sunanta cikin jerin sunayen ministoci da aka yi.
Sai dai daga baya an cire sunanta inda aka maye gurbinta da sunan Mariya Mahmoud Bunkure wacce rahotanni suka tabbatar da cewa kawa ce ga, Amina, ‘yar tsohon gwamnan Kano.
Tsohon gwamnan ya yi shaguben ne a lokacin da Mariya Mahmoud Bunkure ta kai masa ziyara ga tsohon gwamnan domin nuna farin cikinta, inda suka rika ambatar sunan Maryam Shetty tare da tuntsurewa da dariya.
Ita dai Mariya Mahmoud Bunkure ta rike mukamin kwamishina ta Hukumar Manyan Makarantu ta jihar Kano a lokacin mulkin tsohon gwamna Ganduje.
Sai dai wani abu da ya daukar hankali a yayin wannan ziyara shi ne yadda tsohon gwamnan Kanon ya mayar da martani ga masu kiran sunan matarsa, Hafsat Umar Ganduje da aka fi sani da “Gwaggo”.
A cewar gwamnan yana so mutane su cigaba da kiran sunan Gwaggon wanda a ganinsa wannan zai kara tabbatar da wautar masu kalubalantarsa game da cewa uwargidansa ce ke tafi da al’amuransa.
Abin da da yawa daga cikin mutane da su sani ba shi ne, Maryam Shetty da Mariya Mahmoud Bunkure abokai ne tun a makaranta ta Kano Foundation da kuma sake haduwa a jami’ar Bayero a tsangaya daya ta Kimiyya.