Hukumar kashe gobar ta jihar Kano Kar kashin jagorancin darakta janar Alh. Hassan Ahmad Muhd ta gudanar da ayyuka a daukacin ofisoshi 28 da ake da su a fadin jihar nan a cikin watan Juli da ya gabata.
Wannan sanarwa ta fito ne daga jami’in hulda da jama’a na hukumar, PFS. Saminu Yusif Abdullahi.
Ayyukan su ne kamar haka:
- Kiran gobara guda 252.
- Kiran neman agajin gaggawa guda 11.3.
- Kiran karya guda 4.4.
- Dukiya da aka rasa sanadiyar ibtila’in gobar # 14,350,000.5.
- Dukiyar da aka samu nasarar ceratarwa daga ibtila’i daban-daban 31,000,000.6.
A cikin watanni bakwan da suka gabata, an rasa rayukan mutane 3 sanadiyar ibtila’i daban- daban.
Sannan hukumar ta samu nasarar tseratar da rayukan mutane 8 daga ibtila’i daban-daban.
Inda Alh. Hassan Ahmad Muhd ya yi kira ga al’umma da su kula a yayin amfani da wuta don kauce wa ibtila’in gobara, da kuma jan hakali ga masu amfani da tukunyar iskar gas na girki a jikin ababen hawa da na’urar janareto.
Sannan ya jan hankalin al-umma da su gyara magudanan ruwa duba da yanayin damuna da ake ciki da kaucewa faruwar ibtila’in ambaliyar ruwa.