Home » Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Kafa Hukumar Kyautata Wa Talakawa

Majalisar Dattawan Najeriya Za Ta Kafa Hukumar Kyautata Wa Talakawa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da ayyuka na musamman ya yi alwashin yin doka da zata taimaka wajen kafa wata hukuma da zata kyautata wa talakawa da masu karamin karfi, to sai dai masana na ganin akwai abin dubawa domin sauran hukumomin da ake da su ba a tafiyar da ayyukansu yadda yakamata.

Wannan doka dai idan aka yi ta zata tabbatar da dorewar shirin nan na gwamnatin tarayya na tallafa wa marasa karfi da gajiyayyu maza da mata a Najeriya wanda aka fara a shekarar 2016. Shugaban Kwamitin Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, shi ne ya sanar da haka a lokacin taron jin ra’ayoyin jama’a kan kudurin dokar da zata tabbatar da hukumar.

Yusuf ya ce an gabatar da kudurin ne domin ana so a bar wani muhimmin abu bayan wa’adin gwamnati mai ci, saboda an ga alfanun shirin wanda aka kwashi shekaru kusan bakwai ana yi kuma mutane suna samun tallafi.

Yusuf ya ce abu ne mai kyau idan gwamnati mai jiran gado zata ci gaba da shi, shi ya sa za a yi dokar da zata karfafa mata gwiwa ganin cewa aikin gwamnti ne tallafa wa talakawan kasa.

Shugaban shirin tallafa wa talakawa na kasa Dr. Umar Buba Bindir, ya ce mutane da yawa zasu amfana da shirin.

An kasa shirin zuwa bangarori hudu, da farko akwai matasa miliyan daya da dubu dari biyar wadanda basu da aiki, ana koya masu sana’a sannan a basu tallafi.

Akwai kuma yaran talaka da ake ciyar wa a makarantu su miliyan goma zuwa miliyan sha biyu, da mata miliyan uku masu kananan sana’o’i da ake basu bashin kudi dubu hamsin zuwa dubu dari uku, sannan akwai gidaje miliyan biyu da ke dauke da mutane miliyan goma da ake ba su naira dubu 5 domin su samu abinci.

Bindir ya ce shiri ne da ya kamata ya dore amma a karkashin hukuma mai zaman kanta.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?