Masu fashin baƙin kan al’amuran yau da kullum a Najeriya sun yi hasashen cewa kayan masarufi a bana za su yi tsada saboda karancin kudi a hannun al’umma.
Rashin kundin dai na da nasaba da sauyin launin kudi da aka yi a Najeriya, lamarin da ya sa har yanzu hada-hadar kudi ta kasa daidaita a kasar har izuwa yanzu da aka fara azumin watan Ramadan.
Wannan babban kalubale ne musamman idan aka yi la’akari da cewa mafi yawan masu kayayyakin buƙatun yawan da kullum da aka fi bukata a cikin watan ba sa ta’ammali da na’urar zamani ta hada-hadar kudi (POS).
A lokacin azumi dai akan bukaci kayan marmari kamar lemo, mangwaro, kankana, ayaba da sauransu.
Wasu yan kasuwa masu saida kayan marmari, sun ce babu abin da ya canza a farashin kayan marmari kuma suna fatan ba za a samu ƙarin farashi ba.
‘Yan kasuwar dai sun bayyana tsarin hada-hadar kasuwanci ba tare da musayar tsabar kudi ba a matsayin wani babban ci gaba, yayin da wasu ke ganin hakan na kawo naƙasu ga tsarin kasuwanci.
Sai dai mafi akasari ‘yan kasuwar da ke karkara na kokawa kan sabon tsarin kasuwanci ba tare da musayar tsabar kudi ba.