Sabuwar Majalisar Dokokin jihar Neja ta 10 ta gayyaci shugabannin hukumomin tsaro a jihar domin jin bahasi daga wajensu akan matsalar rashin tsaron da ke kara kamari a jihar.
Sabon shugaban Majalisar Dokokin jihar Nejan Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce, a yau Laraban ne za su gana da shugabannin hukumomin tsaron dake aiki a jihar wanda hakan shi ne zaman aiki na farko da za su fara yi bayan kaddamar da majalisar a jiya Talata.
A baya dai an sha zargin ‘yan Majalisun jihohin da zama ‘yan amshin shata ga bangaren gwamnoni bisa la’akkari da yadda suke zama tamkar rakumi da akala a tsakaninsu da banagaren zartarwar.
To sai dai, shugaban Majaliasar Barista Abdulmalik Sarkin Daji ya ce a wannan karon za su hada hannu da bangaren zartarwa wajan kawo ci gaba mai amfani ga Al’umma.