Majalisar Koli ta Darikar Tijjaniyya ta yi kira ga al’ummar Musulmin Najeriya da su mai da hankali wajen yin addu’o’in rokon Allah Ya warware matsalar tsaro da ake fama da ita a wasu sassan kasar nan da kuma tsadar rayuwar da ake ciki yanzu haka.
Bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwar bayan taro dake dauke da sa hannun shugaban kwamitin yada labarai, Malam Ibrahim Inyas Abubakar, da kuma sakataren yada labaran kwamitin majalisar Shura, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa.