An gudanar da Taron saukar karatun Alqur’ani mai girma sau 2,474 a masallacin Khalifa Isiyaka Rabi’u dake Goron Dutse, kamar yadda Shugaban Cibiyar Haddar Alqur’ani ta Sheikh Isiyaka Rabi’u, Musbahu Tijjani Rabi’u ya bayyana mana,
Ya ce an yi saukar ne da nufin nema wa al’ummar musulmi saukin rayuwa a wajan Allah subhanahu wata’ala.
An dai gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin Khalifa Nafi’u Isiyaka Rabi’u.
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya kasance Uban Taron.