Home » Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Bincika Musabbabin Haɗuran Jiragen Ƙasa

Majalisar Wakilan Najeriya Za Ta Bincika Musabbabin Haɗuran Jiragen Ƙasa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta kan harkokin sufuri da ya binciki yawan hatsarin jiragen kasa da yake janyo asarar rayuka da dukiyoyi a fadin kasar nan.

Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da Unyime Idem NA JAM’IYYAR PDP, daga jihar Akwa Ibom ya gabatar wanda ya bayyana cewa jerin haduran jiragen kasa sun yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi a ƙasar.

Ya ce, “A watan Janairun shekarar nan, an samu rahoton wani hatsarin jirgin kasa a Kubwa da ke Abuja wanda ya yi sanadin mutuwar wata mata Selimota Suleiman, ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA.

“A ranar Alhamis 9 ga watan Maris ɗin da muke ciki kuma, wani jirgin kasa ya kutsa kai cikin wata motar safa ta BRT a Jihar Legas, inda ya yi sanadin mutuwar mutum shida tare da jikkata wasu da dama.

“A ranar 28 ga Maris, 2022, an kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna hari kuma ‘yan Najeriya da dama sun rasa rayukansu; yayin da wasu suka samu raunuka sannan aka sace wasu.

Haka kuma, Jirgin ƙasan Warri zuwa Itakpe ya kauce hanya a cikin dajin Kogi, inda aƙalla fasinjoji 300 suka makale. cikin wata guda bayan an sace fasinjoji kusan 20 daga tashar jirgin kasa a Igueben a Jihar Edo”.

Ya ce duk da irin halin da ake ciki na rashin kulawar da wasu ke nunawa, ba a taba dora alhakin faruwar hakan a kan wani ba. Ya kara da cewa: “Wadannan al’amura marasa dadi sun faru sau da yawa saboda ba a dauki matakin hana faruwarsu a gaba ba.”

Don haka majalisar ba da umarnin a binciki musabbabin aukuwar haduran jiragen kasa daban-daban a fadin kasar nan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?