• Home  
  • Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0
- Babban Labari - Wasanni

Man City ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea 1-0

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin FA na shekarar 2026 bayan doke Chelsea 1-0. Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci. Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao […]

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Manchester City ta lashe kofin FA na shekarar 2026 bayan doke Chelsea 1-0.

Antoine Semenyo ne ya zura ƙwallon da ta bai wa Man City nasara bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wannan ne kofi na biyu da ƙungiyar ta lashe a kakar wasa ta bana bayan lashe kofin Carabao a baya-bayan na, inda take harin kofin Firimiya da Arsenal ke kan teburi.

Zuwa yanzu Pep Guardiola ya lashe kofuna 20 cikin shekaru 10 a Manchester City.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000