• Home  
  • An kama wasu mutum 7 da ake zargin ƙusoshin Boko-Haram ne a filin jirgin Katsina
- Babban Labari

An kama wasu mutum 7 da ake zargin ƙusoshin Boko-Haram ne a filin jirgin Katsina

Hukumomin Najeriya sun ce an kama wasu mutum bakwai da ake zargi da kasancewa jiga-jigan a ƙungiyoyin Boko-Haram da ISWAP ne. Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka lokacin sanya hannu kan sabuwar dokar shaidar ɗan ƙasa a Abuja. Mista Tunji-Ojo ya ce an kama mutanen ne a lokacin d asuka […]

Hukumomin Najeriya sun ce an kama wasu mutum bakwai da ake zargi da kasancewa jiga-jigan a ƙungiyoyin Boko-Haram da ISWAP ne.

Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka lokacin sanya hannu kan sabuwar dokar shaidar ɗan ƙasa a Abuja.

Mista Tunji-Ojo ya ce an kama mutanen ne a lokacin d asuka dawo naga aikin Hajji na 2026 a filin jirin saman Katsina cikin makon da ya gabata.

Ministan ya ce an kama mutanen ne bayan bibiyar bayanan mutanen da suka tafi aikin hajji a faɗin ƙasar.

Ya ce yanzu haka mutanen bakwai na hannun hukumar tsaro ta DSS wadda take gudanar da bincike kan lamarin.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai