Home » Manyan Makarantu Sun Tsunduma Yajin Aiki A Adamawa

Manyan Makarantu Sun Tsunduma Yajin Aiki A Adamawa

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Gamayyar ƙungiyoyin manyan makarantu na gwamnatin Jihar Adamawa sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a jiya Talata, 11 ga watan Maris.

Ma’aikatan manyan makarantun da suka haɗa da masu karantarwa da waɗanda ba sa karantarwa sun shiga yajin aiki ne bayan wa’adin yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ya ƙare a jiya Litinin.

Cikin wata sanarwa da shugaba, Maryam Abdullahi da kuma sakataren ƙungiyoyin, Kwamared Musa Yakubu suka sanyawa hannu, sun alaƙanta yajin aikin a matsayin martani da halin ko-in-kula da gwamnatin jihar ta nuna kan buƙatunsu.

Dangane da hakan gamayyar ƙungiyoyin ke kiran dukkan mambobinta da su tsunduma yajin aikin na sai baba ta gani.

Aminiya ta ruwaito cewa, yajin aikin ya shafi manyan makarantu daban-daban ciki har da kwalejojin ilimi da fasaha da na lafiya da ke faɗin Jihar Adamawa.

Ƙungiyoyin dai na neman gwamnatin ta mayar da mambobinsu kan tsarin albashin manyan makarantu da kuma tsarin sabon albashi mafi ƙanƙanta da kuma janye tsarin zaftare albashinsu da ake yi da sunan haraji.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?