Hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kasa, Police Service Commision (PSC) ta amince nadin CP Ibrahim Adamu Bakori, a matsayin sabon kwamishinan yan sandan jihar Kano.
Sabon kwamishinan yan sanda Ibrahim Bakori, shi ne zai maye gurbin, AIG Salamn Dogo Garba , wanda ya samu Karin girma daga kwamishinan yan sanda zuwa mataimakin babban sufeton yan sandan Nijeriya AIG.
Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kula da aiyukan yan sanda na kasa , Ikechukwu Ani, ya fitar a madadin shugaban hukumar , DIG Hashimu Argungu mai ritaya.
Bakori haifaffen jihar Katsina ne a arewa maso yammacin Nijeriya, inda yankin da ya fito ke fama da matsalar yan bindiga da suke garkuwa da mutane tare da hallaka su.
- Shugaba Tinubu Ya Amince Da Sauya Sunan Jami’ar ilimi Ta Tarayya Kano Zuwa Yusuf Maitama Sule.
- Mutum 1 Ya Rasu 21 Sun Jikkata Sanadiyar Fashewar Tukunyar Gas : Yan Sandan Kano
Kafin turo shi jihar Kano , shi ne kwamishinan yan sanda mai kula da sashin binciken laifukan kisan kai , a rundunar yan sanda ta kasa dake Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa , tuni hukumar ta aike da takaddar amincewa ga babban sufeton yan sandan Nijeriya , don aiwatarwa, mai dauke da sa hannun sakataren hukumar, Chief Onyemuche Nnamani.
Argungu ya hori sabon kwamishinan yan sandan ya tabbatar da an samu wanzuwar zaman lafiya a fadin jihar Kano.