A yayin da aka yi bikin ranar ruwa ta duniya ranar 22 ga watan Maris, Najeriya ta shirya wani taro domin bayar da shawarwari ga duk sassan gwamnati da manyan masu ruwa da tsaki a fannin, la’akari da kudirin shawo kan matsalolin da suka shafi ruwa a kasar.
Masu ruwa da tsaki a taron ranar ruwa ta duniya mai taken ”gaggauta kawo sauyi” wanda aka yi a Abuja, sun jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin gwamnati da dukkan masu ruwa da tsaki don samar da yanayi mai dorewa a fannin samun tsaftataccen ruwan sha da na amfanin yau da kullum musamman ga yara, da aikin samar da abinci ga kowa, da la’akari da bukatun ruwa a gidaje da sauran wurare.
A yayin jawabin da ta yi bayan taron na masu ruwa da tsaki, Mrs. Nweke wacce ta wakilci babban sakataren ma’aikatar ruwa ta tarayya, ta ce bikin na bana ya mayar da hankali ne a kan fafutukar gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen linka kokarinsu, da zuba isassun kudadden da ake bukata don aikin samar da tsaftataccen ruwan sha, da samar da kayayyakin aiki, da bada bayanai da kuma kirkire-kirkire don ganin an cimma dukkan amfanin da za a iya samu na ruwa bayan rage yawan matsalolin da ke tattare da rashin tsaftataccen ruwan sha.
A wani bangaren kuma, masani a fannin muhalli da albarkatun kasa da ke aiki tare da hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO, Seyi Fabiyi, ya ce ruwa na da muhimmanci ga manufofin FAO saboda yadda kaso saba’in da biyu cikin dari na janyewar ruwa ana amfani da su ne a fannin aikin noma kuma tsarin abinci ya dogara sosai kan albarkatun ruwa.