Home » Faransa: Al’amura Sun Tsaya Cak Saboda Yajin Aiki da Zanga-zanga

Faransa: Al’amura Sun Tsaya Cak Saboda Yajin Aiki da Zanga-zanga

by Anas Dansalma
0 comment

A yau, Alhamis, al’amura sun tsaya cak a ƙasar Faransa bayan da al’ummar kasar suka shiga yajin aiki da zanga-zangar nuna ƙin dokar fansho da shugaba Emmanuel Macron ya saka.

Zanga-zangar wadda ke gudana a faɗin ƙasar wanda shi ne karo na 9 da kungiyoyin kwadago suka jagoranta tun daga watan Janairu.

A jiya, an kai ruwa rana tsakanin jagororin fansho da shugaba Emmanuel Macron bayan da shugaban ya kafe kan kudirinsa na kara shekarun ritaya zuwa shekaru 64 da ake sa ran dokar za ta fara aiki a cikin shekarar nan.

A yayin ganawar shugaba Macron da kungiyoyin, sun ja hankalinsa kan yadda kudirinsa zai jawo fushin miliyoyin ‘yan ƙasar, sai dai shugaban ya bayyana cewa bashi da shirin ja da baya kan dokar.

Philippe Martinez da ke jagorantar kungiyar kwadago ta CGT ya ce martani daya da za su mayar wa da shugaba Macron shi ne ganin miliyoyin jama’a na zanga-zanga tare da ƙauracewa aikinsu.

Zanga-zangar ta yau ta yi mummunar illa ga ɓangaren sufurin ƙasar, ciki har da tashoshin jiragen sama da na kasa waɗanda suka tsaya da aiki cak sakamakon yadda jami’ansu suka bi sahun masu boren.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?