Home » Masarautar Kano Ta Ɗaga Darajar Wasu Hakimai da Naɗa Wasu Sabbi

Masarautar Kano Ta Ɗaga Darajar Wasu Hakimai da Naɗa Wasu Sabbi

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment

Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi sauye-sauye na daga darajar wasu hakimansa da kuma nada wasu sababbin hakimai.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abubakar Balarabe Kofar-Naisa, Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano ya fitar a ranar Juma’a a Kano.

Ya ce daga cikin hakiman da aka daga darajarsu sun hadar da Sarkin Dawakin Tsakar-Gida, Alhaji Ahmad Ado Bayero zuwa Dan Iyan Kano, sai kuma Turakin Kano, Alhaji Lamido Sunusi Bayero zuwa Sarkin Dawakin Tsakar-Gida.

Sauran sun hada da Tafidan Kano, Alhaji Mahmoud Ado Bayero, wanda ya zama Turakin Kano, yayin da Dan Galadiman Kano Alhaji Haruna Rasheed Sunusi aka daga darajarsa zuwa Tafidan Kano, sai Alhaji Kabiru Tijjani Hashim Dan Isan Kano ya zama Dan Galadiman Kano.

A cewar sanarwar, sauran su ne Dan Lawan din Kano Alhaji Bashir Ado Bayero ya koma Dan Isan Kano, sai Alhaji Yahaya Inuwa Abbas, Dan Majen Kano ya zama Lawan din Kano.

Kazalika, sanarwar ta ce Sarkin ya nada Alhaji Ahmad Kabiru Bayero a matsayin Barde Kerarriya da kuma Alhaji Abdulkadir Mahmoud a matsayin Magajin Rafin Kano.

Da ya ke jawabi jin kadan baya nadin nasu, Sarkin ya ce an basu wannan rawani ne saboda cancantarsu da kuma hidimta wa al’umma. Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci da su zamo jakadu nagari a duk inda suka sami kansu tare da ciyar da Masarautar Kano gaba.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?