Home » Masu Haƙar Kabari Sun Koka Kan Rashin Samun Alawus A Kano

Masu Haƙar Kabari Sun Koka Kan Rashin Samun Alawus A Kano

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Masu haƙa kaburbura da gyara maƙabarta sun koka kan ƙarancin alawus ɗin da ake ba su na naira 3000 a wata.

Wani mai haƙar kabari a maƙabartar unguwar Tudun Wada da ke Kano, Malam Suleiman Mohammed ya shaida wa majiyarmu cewa a wasu lokutan akan biya su ƙasa da naira dubu uku, yayin da mafi yawan alawus ɗin da aka ba su a shekarun baya bai wuce naira 5,000 ba.

Mutumin wanda ya kwashe shekara sama da 30 yana aikin haƙa kaburbura a maƙabartar, ya ce sun kai kukansu gaban Sarkin Kano don nema a ƙara musu alawus-alawus, inda aka yi musu alƙawarin za a duba.

Ya ce tun da fari ana biyan su naira 1,000 ne kacal, kafin a yi musu ƙarin ya kai 5,000 kuma a halin yanzu ya koma naira 3,000 ko 2,500.

A cewarsa wani lokacin akan ɗauki watanni ba a ba su alawus ɗin ba.

“Aikin haƙa kabari abu ne mai wuya,” in ji malam Suleiman “saboda hatsarin da ke tattare da hakan, kuma aiki ne na ƙarfi da ke sanya ciwon jiki, don haka ko nawa za a biya su ba zai yi yawa ba.”

Mai haƙar kabarin ya koka kan yadda wasu ɓata gari ke amfani da maƙabartar wajen adana makamai ko shaye-shaye, lamarin da kan janyo gobara a maƙabartar.

Yayin da a wasu lokutan wasu kan je maƙabartar domin yin abubuwan da suka shafi tsubbace-tsubbace.

Ya nemi a inganta ayyukansu ta hanyar tsaftace maƙabartar da gyara katangarta da sanya fitulu.

Ana amfani da maƙabartar wajen binne mamata daga kimanin unguwanni goma, lamarin da ya sa a yanzu ta cika, sai an lalubo tsohon kabari kafin a binne sabuwar kushewa.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?