Home » Bikin Sallah: Yan Kasuwar Kantin Kwari Sun Koka Da Rashin Ciniki

Bikin Sallah: Yan Kasuwar Kantin Kwari Sun Koka Da Rashin Ciniki

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Daga : Shareep Khaleepha Sharifai

Yan kasuwar kantin Kwari a jihar Kano, masu siyar da Yadi, Shadda, Atamfofi da Abaya da dai sauransu , sun koka sosai kan yadda ciniki  yaja baya ,duk da cewa a irin wannan lokaci na karatowar bikin sallah suna samun karuwar masu cinikin kaya suke shigo wa daga sassa daban-daban na Nijeriya harma da makotan kasashe.

Wasu daga cikin yan kasuwar sun shaida wa wakilin mu cewa , a kowacce shekara, makonni biyu kafin gudanar da bukukuwan sallah, sukan samu karuwar mutanen suke shigowa kasuwar don siyan kayan sallah ,amma a wannan shekarar kayan nasu yana nan a jibge babu masu siya da yawa.

Sai dai wani dan kasuwa ya alakanta karancin cinikin da yadda wasu daga cikin al’umma suka koma siyan dinkakkun kaya, saboda saukin da suke samu duk da cewa suma Telolin sun koka saboda tsadar kayan.

Haka zalika sun ce karuwar farashin kayayyakin da kaso 25 cikin 100 na daga cikin dalilan da suka Sanya al’umma basa iya zuwa kasuwar don siyan kayan.

Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na ganin rashin kudi a hannun al’umma ne ya hanasu siyan kayan da kuma matsin tattalin arziki da kasar fuskanta.

A karshe yan kasuwar sun yi kira ga gwamnati da ta lalubo hanyoyin warware matsalar da harkokin kasuwancin ke fuskanta don samarwa yan Nijeriya sauki.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?