Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka Kamala Harris ta bayyana cewa samun ƙarin mata a kan karagar mulki a matsayin wani muhimmin tubali na kafa ingantacciyar dimokaradiyya.
Wannan ziyara na zuwa ne a daidai lokacin da fadar White House ta Amurka ke gudanar da taron ƙoli na dimokaridiyya karo na biyu a birnin Washington.
Harris ta ce domin samar da ingantaccen tsarin dimokuradiyya, akwai buƙatar ba wa mata damar riƙe madafun iko tare da sanya hakan ya zama ruwan dare gama duniya, ba wai wani abu da zai zama na kwatance ba.
Sannan da ta gana da mata ‘yan kasuwa da shugabanni a babban birnin kasar Ghana, inda ta yi shelar bayar da Tallafin haɗin guiwa tsakanin Gidauniyar Bill da Melinda Gates da gwamnatin Amurka na dala biliyan ɗaya ga kamfanoni masu zaman kansu don ciyar da tattalin arziki mata gaba a Afirka.