Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya ta ce Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kai samame ofishin su da ke Abuja.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta kafar X ta zargi jami’an tsaron da yi wa ofishinsu ƙawanya ba bisa ka’ida ba.
SERAP ta ce bayan kawanyar da jami;an na DSS su ka yi wa ofishin nata, sun bukaci ganawa manyan daraktocin ta.
SERAP ta yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya shiga tsakani kuma ya umarci jami’an DSS ta daina abin da ƙungiyar ta kira ”tsangwama da cin zarafi, da kuma take haƙƙin ‘yan Najeriya”.