Mai ba wa shugaba Tinubu shawarwari kan lamuran siyasa Ibrahim Kabir Masari ya ce wasu ‘yan damfarar siyasa na karbar kudi daga hannun wasu da sunan za su sa shugaba Tinubu ya nada su Ministoci.
Ibrahim Masari wanda Shugaba Tinubu ya nada shi mai ba da shawara kan siyasa a cikin sabbin mukaman mataimaka 14 da ya fitar, ya ce akwai wadanda ke karbar takardun kwarewar aikin mutane da yaudarar za su kai hukumar DSS da EFCC don tantancewar samun mukamai.
Da ya ke magana kan wani jerin sunayen mutane da a ka fito da shi ranar litinin da ke nuna wadanda a ka nada ministoci da hakan bai tabbata ba, Masari ya ce masu gaggawa ne su ka aikata haka da kuma masu marawa wasu baya.
Babban dan siyasar gwamnatin Tinubun ya ce in Tinubu ya dawo zai bayyanawa duniya jerin sunayen ministocin ko kuma za a ji jawabi daga bakinsa