Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gargadi manyan kasashen duniya game da ci gaba da sace albarkatun nahiyar Afirka.
Ya yi gargadin ne a jawabin da ya gabatar a wurin taron shugabannin Afirka da aka yi a Nairobi babban birnin Kenya ranar Lahadi.
Ya yi wannan jawabi ne a yayin da manyan kasashen duniya ke ci gaba da gogayya da juna domin yin tasiri a Afirka abin da masana ke gani wani bangare ne na tatsar albarkatun kasar nahiyar.
Shugaba Tinubu ya yi tir da wannan sabon tsari na neman gindin zama a Afirka, inda ya yi kira ga kasashen nahiyar su hada kai domin cimma manufa iri daya.