• Home  
  • Mutane 10 sun Rasu A Wajen Haƙo Zinare A Zamfara
- Babban Labari - Labarai

Mutane 10 sun Rasu A Wajen Haƙo Zinare A Zamfara

A Najeriya, ana can ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wani wurin hakar ma’adinai da ya rufta da mutane da dama, a kauyen Kadauri na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara. Zuwa yanzu dai an ciro gawarwakin mutum goma, wasu hudu zuwa biyar kuma suka tsira da munanan raunuka. Alhaji Bello […]

A Najeriya, ana can ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a wani wurin hakar ma’adinai da ya rufta da mutane da dama, a kauyen Kadauri na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Zuwa yanzu dai an ciro gawarwakin mutum goma, wasu hudu zuwa biyar kuma suka tsira da munanan raunuka.

Alhaji Bello Muhammad Ja-Baka, shi ne shugaban karamar hukumar ta Maru, ya tabbatar wa BBC da aukuwar lamarin, inda ya ce ƙasa ce ta zaftare sanadiyar mamakon ruwan sama da aka yi a yankin.

“Su kuma aikin haƙo zinaren ba bisa ƙa’ida ba, ba su yi la’akari da yanayin ruwan ba sai suka ci gaba da aiki, hakan ya sa ƙasar ta rufta da su,” in ji shi, sannan ya ƙara da cewa ana ci gaba da tuna ƙasar da tunanin akwai wasu a ciki.

Ya ce gwamnati a shirye take da tabbatar duk masu aikin haƙo zinare sun samu lasisi a wajen gwamnati da kuma wajen jami’an tsaro.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai