Mutane 2 Sun Rasu Wasu Sun Jikkata A Mummunan Hatsarin Mota A Kano

Hukumar kiyaye hadura ta kasa reshen jihar Kano, ta tabbatar afkuwar Wani mummunan hadari tsakanin wasu motoci 2 da kuma babur kirar Jinchang aka titin Airport
road Kano.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:15am ba safiyar ranar Laraba.

Kakakin hukumar na jihar Kano, CRC Abdullahi Labaran , ya tabbatarwa da manema cewa mutane shida ne lamarin ya shafi, Inda mutane 2 suka Rasu nan take, ya yin da mutum 1 ya samu raunuka sai kuma sauran mutane ukun da suka tsallake rijiya da baya.

Labaran ya kara da cewa rashin ka’idar tuki ce ta haifar da mummunan hatsarin Tsakanin motar kirar DAF da kuma babur kirar Jincheng.

Bayan faruwar lamarin jami’an hukumar FRSC suka garzaya wajen tare da kai tare da Wanda ya samu raunukan zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammed don bashi kulawar gaggawar, ya yin da mutane biyun da suka rasu aka kaisu asibitin Malam Aminu Kano, don tabbatar da rasuwarsu.

Abdullahi Labaran ya ce dukkan motocin da sauran kayayyakin da aka samu an mika su , ofishin yan sanda na Gwagwarwa don gudanar da bincike.

Kwamandan hukumar reshen jihar Kano, Umar Mas’udu Matazu, ya mika sakon ta’aziyarsa ga iyakan wadanda suka rasa rayukan su da kuma addu’a da fatan Samun sauki ga wadanda suka samu raunuka.

A karshe hukumar ta yi kira ga al’umma da su ci gaba da yin tuki cikin nutsuwa da bin dokokin hanya don kaucewa afkuwar hadura.

Post masu alaƙa

An kashe mutum saboda Naira 200 a Ogun

Masu ruwa da tsaki na APC a jihar Akwa Ibom sun yi watsi da tsarin tsayar da ɗan takara ta maslaha

Makarantar kurame ta Katsina ta lashe gasar wasannin guragu ta gwamna Radda