Wasu mutum bakwai sun rasa ransu sakamakon hatsarin kwale-kwale lokacin da suke tafiya daga kauyen Gidan Husaini zuwa Gwargawu na karamar hukumar Shagari a jihar Sakkwato ranar Litinin.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da mamatan ke tafiya a wani kogi, lamarin da ya jefa mutanen yankin cikin jimami da alhini.
Ba a dai bayyana sunayen wadanda suka rasun ba, amma hukumomi a yankin sun tabbatar da cewa dukkan mamatan ’yan asalin kauyen na Gidan Husaini ne.
- Ambaliya : Kungiyoyi Sun Bukaci Gwamnatin Nijeriya Ta Diyyar Wadanda Iftila’in Mokwa Ya Shafa
- Tinubu Ya Karrama Bill Gates Da Lambar Yabo Ta CFR
Da ya jagoranci wata tawagar gwamnatin jihar domin yin ta’aziyyar mamatan, Kwamishinan Kudi na jihar, Muhammadu Jabbi Shagari, ya bayyana hatsarin a matsayin rashi ga ilahirin mazauna yankin, jihar da ma al’ummar Musulmi baki daya.
Sai dai Kwamishinan ya yi kakkausan gargadi ga matuka kwale-kwalen a kan yin lodin da ya wuce kima, inda ya ce rayuwar mutane ta fi komai za a samu muhimmanci.
Sai dai hatsarin ya sake fito da damuwar da ake da ita kan harkar sufuri ta ruwa a yankunan karkarar jihar, inda mutane suka dogara da kwale-kwalen saboda karancin jiragen ruwa.