Rundunar yan sandan jihar Kano, ta tabbatar da gano bindiga kirar AK-47 ta bogi, a gidan daya daga cikin wadanda ake zargi da halaka baturen yan sandan Rano CSP Ali Baba.
Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook, inda ya ce an samu bindigar ce lokacin da aka tsaurara bincike a gidan mutumin.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan da kisan da aka yi wa Baturen yan sandan Rano, bayan da wasu matasa suka farmaki ofishin yan sandan tare da yin barna da kuma kone motoci guda biyu.
- Mutane 7 Sun Rasu A Hatsarin Kwale-kwale A Sokoto
- Ambaliya : Kungiyoyi Sun Bukaci Gwamnatin Nijeriya Ta Diyyar Wadanda Iftila’in Mokwa Ya Shafa
Idan ba a manta ba, matasan da ake zargi da aikata aika-aikar sun zargi jami’an yan sandan Rano da kisan kan wani matashi mai suna Abdullahi Musa , bayan sun kama shi bisa zarginsa da yin guje-guje da tukin ganganci akan babur.
Sai dai ruundunar yan sandan jihar ta ce lokacin da aka kama matashin , sai ta gano ya fara nuna wasu alamu na gajiya da rashin kwarin jiki , inda ta kaishi babban asibitin Rano, kuma washegarin ranar ya rasu lokacin da yake samun kulawar likitoci.
Tuni rundunar ta sanar da cafke mutane 41 wadanda ake zargi da hannu wajen aikata laifin.

