Kungiyar Likitocin Zuciya da Huhu ta Ƙasa (ACTSON) ta ce sama da mutane 80,000 ne suke bukatar a yi musu aiki sakamakon kamuwa da ciwon zuciya kowacce shekara a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar, Dokta Uvie Onakpoya, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Abuja, yayin babban taron kungiyar na shekara-shekara karo na biyar.
Ya lura cewa ciwon zuciya na kan gaba wajen kisan mutane a duniya, kuma adadin wadanda ke mutuwa a sakamakon shi ya haura na dukkan ragowar cututtuka baki daya.
Dokta Uvie ya ce yayin da wasu daga cikin nau’ukan cutar da su ake haifar mutum da su, wasu kuma a kan kamu da su ne dalilin kwayoyin cuta da yanayin rayuwa da hawan jini da dai sauran dalilai.
A yayin taron, Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari, wacce hadimarta, Dokta Victoria ta wakilta, ta ce a kwanan nan, ta dauki nauyin aikin zuciya ga yara 10 da kuma manya 13.