Akalla mutane 80,000 ne suka rasa matsugunansu a cikin watanni uku sakamakon rikicin kabilanci da ya barke a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, kamar yadda wani jami’in yankin ya ce, yayin da sojoji ke kara karfafa tsaro domin kawo karshen rikicin.
Tun a watan Mayun da ya gabata ne jihar Filato ta fuskanci yawaitar hare-hare a tsakanin Musulmai makiyaya da kuma al’ummar Kiristoci manoma, a rikicin da karamar hukumar ta ce ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 300.
Ko da yake Babban hafsan hafsoshin sojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, ya ziyarci Mangu da ke jihar Filato a ranar Asabar domin fara gudanar da ayyuka na musamman don kawo karshen rikicin.
Gundumar Mangu na daya daga cikin wuraren da rikicin baya-bayan nan ya barke inda aka yi ta sace-sace a kauyuka tare da lalata filayen noma.